Ba mu muka kai wa Burutai hari ba — Zakzaky

Hakkin mallakar hoto non
Image caption El-Zakzaky ya ce babu hannun mabiyansa kan kai hari a kan Burutai.

Kungiyar 'yan uwa Musulmi mabiya mazhabar shi'a a Najeriya, ta musanta zargin kokarin halaka shugaban dakarun kasar Laftanal Janaral Tukur Yusuf Buratai.

Kungiyar a ta bakin shugabanta Sheikh Ibrahim El-Zazzaky na cewa, babu wani daga cikin mutanenta da ya yi kokarin kai hari ga wani Soja, ballantana ma shugaban na Sojoji.

Kungiyar na cewa har yanzu ba ta tantance mutanen da aka halaka da kuma raunata mata ba a wani hari na babu gaira babu dalili yayin bikin canza Tuta da su kan yi duk shekara.

Rundunar ta Sojojin na Najeriya ce dai ta shaidawa BBC cewa mabiya mazhabar Shi'a sun yi kokarin halaka Laftanal Janaral Buratai a wata arangama a Zaria.