Sojoji sun kama El-Zakzaky

Hakkin mallakar hoto non
Image caption Sheikh Ibrahim Al Zakzaky

A Najeriya, sojojin kasar sun kama shugaban kungiyar 'yan uwa Musulmi da aka fi sani da 'yan Shi'a, bayan sun yi wa gidansa kawanya a garin Zaria da ke arewacin kasar.

Wata diyar Sheikh Ibrahim Al Zakzaky ta shaida wa BBC cewa ba ta da masaniya game da inda aka tafi da mahaifinta.

A wayewar garin ranar Lahadi, an yi ta jin karar harbe-harben bindiga da fashewar abubuwa, bayan sa-in-sar da sojojin kasar suka yi da mabiya mazhabar ta Shi'a.

An kashe da dama daga cikin mabiya mazhabar ta Shi'a, sannan aka rusa gidan jagoran nasu.

Sojojin kasar sun zargi kungiyar ta Shi'a da yunkurin halaka babban hafsan sojin kasar lokacin da yaje Zaria ranar Asabar, sai dai kungiyar ta musanta wannan zargi.

Kasar Iran - wacce ke goyon bayan kungiyar Shi'a a Najeriya - ta yi kiran a kwantar hankali.