Burundi: Amurka ta gargadi 'yan kasarta

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Amurka ta gargadi 'yan kasarta game da Burundi saboda ci gaba da kashe - kashen da ake yi aka kasar

Ma'aikatar kula da harkokin kasashen waje ta Amurka ta gargadi 'yan kasar da kar su je Burundi.

Wannan gargadi ya zo ne sakamakon kazancewar fadace-fadace masu nasaba da siyasa a kasar.

A sanarwar da ma'aikatar kula da harkokin kasashen waje ta fitar a ranar Lahadi, ta yi kira ga Amurkawa da ke zaune a Burundi da su fice ba tare da bata lokaci ba.

Tuni dai ma'aikatar ta bayar da umarnin kwashe iyalan ma'aikatan gwmanatin Amurka da kuma ma'ikatan da ba na gaggawa ba a kasar.

Ma'aikatar ta kuma shawarci 'yan kasar wadanda fada ya rutsa da su, da su zauna a cikin gidajen su, su guji zama a gidan sama da kuma kauracewa bakin tagogi da kofofi.

A watan da ya wuce ne Belgium ta ba 'yan kasarta shawarar da su fice daga Burundi, yayin da Tarayyar Tura EU ta rage yawan ma'aikatan ta da ke kasar.

A ranar Juma'a ce aka kashe mutane 87 bayan da aka kai wani hari a wani wurin da sojoji suke, a cewar rundunar sojojin Burundi

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amurka ta yi kira da a gudanar da bincike.

An soma tarzoma a Burundi ne a watan Afrilu bayan da shugaban kasa Pierre Nkurunziza ya sanar da cewa zai tsaya zabe a karo na uku.