Yarjejeniyar sauyin yanayi ta karɓu

Hakkin mallakar hoto Getty

Kwana guda bayan kasashe kusan dari biyu sun amince da yarjejeniyar yaki da sauyin yanayi tuni gwamnatoci suka soma duba yadda zasu aiwatar da yarjejeniyar.

Amma masana kimiyya sun yi gargadin cewa, abinda aka tsaida domin rage dumamar yanayi ba zai isa ba wajen cimma yunkurin rage zafin da duniya take kara yi.

Wata kungiyar cibiyoyin dake bincike kana sauyin yanayi ta ce, kamata yayi dukkan gwamnatoci su tashi tsaye wajen ganin an rage dumamar yanayi cikin shekaru masu zuwa.

Dukkan kasashe dake da alhakin gurbata yanayin duniya sun yi maraba da yarjejeniyar da aka cimma.

Wani kakakin gwamnatin China yace, lamarin ya yi daidai wajen tabbatar da kowacce kasa ta yi abinda ya dace.