Rikici a wasan kalankuwar mawaka a Kaduna

Mawakin Hausa mai suna Kahutu Rarara Hakkin mallakar hoto Rarara
Image caption Mawakin Hausa mai suna Kahutu Rarara

Rahotanni daga garin Kaduna da ke arewacin Nigeria sun ce an sami tashin hankali a wurin kalankuwar mawaka da makada da aka kammala da yammacin ranar Asabar.

Wasu matasa ne dai suka tada rikici yayin da aka dakatar da wata mawakiya daga shiyyar kudancin kasar ci gaba da waka inda aka ba wani mawaki mai suna Kahutu Rarara ya fara ta sa wakar.

An dai yi ta guje guje da turmutsutsu yayin da jami'an tsaro suka yi amfani da Barkonon tsohuwa wajen tarwatsa matasan da suka juya al'amarin zuwa zanga zanga da kai hari ga jami'an tsaro.

Babu tabbacin samun rasuwa to amma mutane da dama sun sami raunuka.

Gabanin wasan kalankuwar wasu 'yan siyasa da kuma malaman addini suka soki lamarin, suna cewa, ganin irin halin da talakan Najeriya yake ciki bai kamata a yi irin wannan taro ba na sheke aya.