Ana tattaunawa kan rikicin Libya

'Yan tawaye a Libya
Image caption Libya ta shiga rikita-rikitar siyasa ne tun bayan hambarar da gwamnatin shugaba Mu'ammar Gaddafi

A yau ne ake gabatar da wani taron kasa da kasa a kasar Italia da nufin tattauna hanyoyin da za a bi dan kawo karshin yakin da ake yi a kasar Libya.

A bangare guda kuma ana nuna damuwa kan cewa mayakan jihadi na kungiyar IS na kokarin kafa sansaninsu a kasar.

Ministocin harkokin wajen kasashen yammacin duniya da na gabas ta tsakiya za su matsa lamba dan a samar da gwamnatin hadaka a Libya, wanda hakan zai bude kofa ga kasashen duniya su tallafawa Libya magance matsalolin da sukai mata dabaibayi.

Tun bayan hambarar da gwamnatin Shugaba Mu'ammar Gaddafi kasar Libya ta fada rikita-rikitar Siyasa.