Sojoji sun rushe gidan Sheikh El Zakzaky

Rahotanni daga garin Zaria a jahar Kaduna na nuna cewa kura ta dan lafa bayan da aka shafe daren Asabar da kuma ranar Lahadi ana rikici tsakanin sojoji da kuma 'yan kungiyar Islamic Movement,wato kungiyar 'yan uwa Musulmi yan mazhabin shi'a da Sojoji.

Har yanzu dai ba a bayyana adadin mutanen da suka jikkata ko suka rasu a harbe harben da aka kwashe tsahon lokaci ana yi a unguwar Gyallesu da kuma Husainiyya masallacin shugaban kungiyar Sheikh Ibrahim El Zakzaky.

Wasu majiyoyi daga Zariyan sun shaida wa BBC cewa tuni Sojoji suka rushe gidan na Sheikh Alzazzaky da kuma masallacin na Husainiyya.

Rahotanni na cewa, an kashe mukaddashin jagoran 'yan Shi'a a Najeriya Malam Muhammadu Turi.

Kafin dai kisan Malam Turi shi ne ke jagorantar 'yan Shi'a a Kano.

Rundunar sojan Najeriya ta zargi 'yan Shi'a da kokarin halaka babban hafsan su Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai yayin wata ziyara a Zaria.

Amma 'yan Shi'a sun musanta zargin da sojan Najeriyar suka yi.