Mace ta lashe zaben gunduma a Saudiyya

Wata mace a kasar Saudiyya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan shi ne karon farko da Mace ta tsaya takara a kasar Saudiyya.

A karon farko a tarihin kasar saudiyya an zabi mace a zaben gundumomi da aka yi a kasar.

Hukumar zaben kasar ta bayyana cewar Salma Bint Hizab al-Oteibi ta yi nasarar zama 'yar majalisar yankin Makkaa.

Inda ta samu kuri'u masu rinjaye kan abokan hamayyar ta maza bakwai da mata biyu.

Kusan mata 1000 ne suka fito takara a wannan karo a kasar Saudiyya, da maza kusan 6000 duk da cewar matan ba su da cikakken iko.

Zaben da aka gudanar a jiya asabar dai shi ne karon farko da mata suka ta ka rawa a matsayin 'yan takara da kuma kada kuri'a.

Ana sa ran za a sanar da sakamako na karshe kan zaben kafin daren yau.