Africa ta kudu ta nada ministan kudi na 3 a mako 1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban Africa ta kudu Jacob Zuma

Shugaba Jacob Zuma ya sanar da nadin Pravin Gordhan a matsayin ministan kudi wanda shi ne na 3 da aka nada a mako guda

Kudin kasar Rand ya yi faduwar da bai taba yi ba bayan da aka bayar da sanarwar sallamar Nhlanhla Nene daga mukamin mistan kudin kasar a ranar Laraba, inda kuma aka maye gurbinsa da David Van Rooyen.

A wata sanarwa da aka fitar a daren Lahadi, Mista Zuma ya ce gwamnatinsa ta saurari ra'ayin jama'a ta kuma yi aiki da ra'ayinsu.

Jam'iyyun adawa sun nemi shugaba Zuma da ya sauka daga mukaminsa ko kuma jam'iyyarsa ta ANC ta yi masa kiranye