Shugabar kamfanin Yahoo ta haifi 'yan biyu

Image caption Shugabar kamfanin Yahoo Marissa Mayer

Shugabar kamfanin aikawa da sakonnin email na Yahoo, Marissa Mayer ta haifi 'yan biyu a ranar Alhamis da safe.

A wani sako da ta aika ta shafinta na intanet, Mayer ta ce "mijina Zack tare da ni, muna farin cikin sanar da ku mun samu karuwar 'yan biyu mata, kuma dukkan mu, muna cikin walwala".

Ana sa rai Mayer za ta tafi hutun haihuwa na karamin lokaci.

Ms Mayer da mijinta Zachary Bogue suna da yaro mai shekaru 3, Macallister.

Bayan ta haifeshi, hutun makonni biyu kadai ta yi, abin da ya haifar da cecekuce, inda wasu ke zarginta da yunkurin bullo da tsarin aiki mara kyau ga iyaye mata a kamfanin Yahoo.

Kamfanin ya na ba da hutun makonni 16 ne ga wadanda suka haifu.