Sojoji sun yi wa gidan El zakzaky kawanya

Dakarun Sojin Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rundunar Sojin Najeriya dai ta zargi mabiya darikar Shi'a da kai harin.

Rahotanni daga Zaria da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya na cewa an kwana ana jin karar harbe-harben bindiga a unguwar Gyallesu da kewaye.

Rahotanin sun kuma ce sojoji sun yi wa gidan shugaban mabiya kungiyar 'yan uwa musulmi ta shia'a Sheik Ibrahim El zazaky da kuma wasu mabiya da ke Husainiyya kawanya .

Rikicin dai ya fara ne tun ranar Asabar lokacin da Babban hafsan rundunar sojin kasa ta Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai ya je wucewa ta kusa da inda mabiya Shi'ar ke taro a cibiyar Husainiyya, inda aka tsare masa hanya, tare da kai masa hari.

Haka kuma rundunar sojin Najeriya ta zargin mabiya kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Shi'a da kai harin, amma sun musanta.

Wannan kawanyar da aka yi wa mabiya shi'ar ta sa 'yan uwansu da ke wasu jihohin Najeriya shiga zanga-zanga a Kano da Katsina.