Al'amura na ci gaba da tabarbarewa a Zaria

Sheikh Ibrahim Zakzaky Hakkin mallakar hoto non
Image caption Sojojin Najeriya sun zargi 'yan Shi'a da kai mu su hari.

Alamurra na ci gaba da tabarbarewa a Zaria da ke jahar Kaduna, tun jiya da aka sami tashin hankali tsakanin Sojoji da kuma yan kungiyar Islamic Movement mabiya mazhabar Shi'a.

Mazauna Unguwar Gyallesu inda gidan shugaban kungiyar Sheikh Ibrahim Alzazzaky yake, na bayanin yadda suka kwashe tsahon daren jiya su na jin karar harbe-harbe babu kakkautawa, ya yin da unguwar ta zama ba shiga ba fita.

Har wayau, Mazauna Unguwar na cewa suna ganin wasu wadanda suke kyautata zaton 'yan Shi'a ne na wuce gidajen su a guje wasu daga cikin su jina-jina.

Rundunar Sojin kasar wacce a yanzu ke fafatawa da yan kungiyar ta Islamic Movement, ba su yi karin bayani a bisa abinda ke faruwa ba.

Sai dai wasu bayanai na nuna cewa Sojojin na kokarin dannawa zuwa gidan Sheikh Alzazzaky ne a yayin da su kuma yan kungiyar ke kokarin kare shi.

Mun yi Kokarin samun Sheikh Alzazzaky ta waya sai dai hakan ya ci tura, to amma yar sa mai suna Suhaila ta shaidawa BBC cewa tun daren jiya ba su san inda Mahaifin na ta ya ke ba, ta kuma tabbatarwa da BBC hare-haren dake gudana a gidan na Sheikh Alzazzaky da kuma tabbatar da cewa mataimakin shugaban kungiyar Malam Turi ya rasu a arangamar dake gudana tsakaninsu da Sojoji.

A nata bangaren Gwamnatin jahar Kaduna ta fitar da wata sanarwa wacce ke kira ga jama'ar jahar da su kwantar da hankulan su. Sanarwar ta ce gwamnan Jahar Mal Nasiru El Rufai ya yi magana da Sheikh Alzazzaky da kuma shugaban sojin na Najeriya Lt Janaral Tukur Buratai tun jiya, haka kuma tun jiyan aka kara tsaurara tsaro a Zaria,to amma babu wata sabuwar sanarwa a bisa abinda ke faruwa a yau.

Bayanai na nuna cewa a ya yin da ake ci gaba da samun matsaloli a Zaria, yan kungiyar ta 'yan uwa Musulmi na gudanar da wata zanga-zanga a kaduna, inda suka nufi gidan gwamnatin jahar.

Ga Badariyya Kalarawi da karin bayani cikin murya:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti