Me ya sa aka jefi Adam A. Zango a Kaduna?

Image caption Adam A. Zango ya bai wa 'yan Kaduna hakuri.

Rahotanni na cewa matasan da suka jefi fitaccen dan wasan fim din nan na Hausa, Adam A. Zango a Kaduna, sun jefe shi ne saboda zargin da suka yi masa cewa ya ce 'shi ne ya koya wa 'yan Kaduna' yadda ake sanya kaya a jiki su yi kyau.

Lamarin dai ya faru ne a wajen kaddamar da bikin kalankuwa, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya halarta a karshen makon jiya.

A lokacin dai an bai wa makada da mawaka damar nishadantar da mutanen da suka halarci kaddamar da bikin.

Sai dai wasu da suka halarci wajen sun shaida wa BBC cewa matasa sun rika yi wa Adam A. Zango ihu a lokacin da aka ba shi damar yin waka.

A cewar su, dan wasan fim din, wanda kuma mawaki ne, ya yi ta kokarin kwantar musu da hankali amma suka ki yarda, suna masu kira a gare shi da ya nemi afuwarsu bisa kalaman da ya yi kafin su bahi ya yi waka.

Daga bisani dai dan wasan ya ba su hakuri, kuma ya samu damar yin wakar da ta kayatar da mahalarta bikin.

BBC ta tuntubi Adam A. Zango domin jin karin bayani amma kawo yanzu bai mayar da martani ba.