Kamaru ta dakile harin Boko Haram

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dakarun Kamaru sun ce sun hallaka mutum daya daga cikin maharan

Gwamnatin Kamaru ta ce jami'an tsaron kasar sun murkushe wani yunkurin kai harin kunar bakin wake a garin Kolofata da ke lardin arewa mai nisa.

Kakakin Gwamnati, Issa Tchiroma Bakary wanda ya ba da tabbacin, ya kara da cewa 'yan kunar bakin waken biyu sun shigo daga Najeriya da misalin karfe 04:30 gabannin sallar asubahi suka kuma doshi masallacin garin da niyyar tayar da ababan fashewar da suke dauke da su.

Sai dai kuma hakarsu ba ta cinma ruwa ba inda ayarin masu tabbatar da tsaro da ake kira 'yan kato da gora suka harbe daya daga ciki da kibiya.

Bayanai sun ce daya dan kunar bakin waken kuma ya gamu da ajalinsa a hannun jami'an tsaro.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar dubban mutane a Nigeria da Chadi da Kamaru da kuma Nijar.