Dasuki na fuskantar sabuwar tuhuma a Kotu

Image caption Dasuki na tsaka mai wuya

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro Sambo Dasuki da wasu mutane uku a gaban kotu a Abuja, a kan wasu sababbin tuhume-tuhume 19 da suka shafi zamba.

A gurfanar da Dasuki tare da Shuaibu Salisu, da ?Aminu Baba-Kusa da kuma wasu kamfanoni bisa zargin sace kudaden al'umma.

Ana zargin su ne da karkatar da fiye da naira biliyan 13 daga asusun gwamnati, amma dukkansu su musanta wannan zargin.

Mai shari'a Hussein Baba Yusuf ya dage sauraron kasar zuwa ranar Talata domin duba batun beli.

EFCC na zargin wadandan mutanen ne rarrabar da kudaden gwamnati ga 'yan jam'iyyar PDP a lokacin zaben fitar da gwani a lokacin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yana neman PDP ta tsayar da shi takara.