Iran ta bukaci Nigeria ta kare 'yan Shi'a

Hakkin mallakar hoto MEHR
Image caption El-Zakzaky na da mabiya a Nigeria

Iran ta bukaci gwamnatin Nigeria ta dauki "matakan gaggawa da suka dace" domin kare 'yan Shi'a a kasar, bayan da sojoji suka hallaka wasu da dama.

Wata kafar yada labarai a Tehran mai suna Tasnim, ta ce Iran ta damu matuka kan matakan da sojoji suka dauka a kan 'yan Shi'a.

"Abin damuwa ne kuma ya kamata a dauki matakan kwantar da kurar rikicin," in ji ministan harkokin wajen Iran, Mohammad Zarif wanda aka ambato ya gayawa takwaransa na Nigeria, Geoffrey Onyeama.

Kawo yanzu dai Nigeria ba ta mayar da martani ba kan wannan rahoton.

Kungiyar Islamic movement ta 'yan Shi'a a Nigeria, ta yi zargin cewa sojoji sun hallaka 'daruruwa' daga cikin mabiyar kungiyar a Zaria, sai dai wasu rahotannin sun ce mutane kusan 20 aka kashe.

Sojojin kasar sun zargi kungiyar ta Shi'a da yunkurin halaka babban hafsan sojin kasar lokacin da ya je Zaria ranar Asabar, sai dai kungiyar ta musanta wannan zargi.

A yanzu haka dai shugaban 'yan Shi'ar Ibraheem El-Zakzaky na hannun jami'an tsaro.