An kashe mutane 14 a kauyen Jos

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jihar Filato ta yi kaurin-suna wajen rikice-rikicen kabilanci da addini da kuma siyasa.

Rahotanni daga jihar Filato ta Najeriya na cewa an kashe mutane 14, sannan aka jikkata mutane biyu a wani hari da aka kai a kusa da Jos, babban birnin jihar.

Lamarin ya auku ne a kauyen Kwata-Zawan ranar Lahadi da daddare lokacin da wasu 'yan bindiga suka kutsa kai cikin wasu gidaje, kana suka harbe mutanen da ke ciki.

Har yanzu dai babu cikakken bayani kan ko su wanene suka kai harin da kuma dalilin da ya sa suka kai shi.

Sai dai wani dattijo a kauyen Mista Gregory Gong, ya shaida wa BBC cewa an binne mutanen da suka mutu.