Zan kawo ci gaba a Kanywood — Rashida

Hakkin mallakar hoto Rashida
Image caption Rashida a yanzu ta zama mai ba gwamnan Kano shawara kan harkokin mata

Fittacciyar jarumar fina-finan Hausa Rashida Abdullahi ta ce nadin da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi mata a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin mata, babbar nasara ce ga masu shirya fina-finan Kanywood.

A hirar da ta yi da BBC Rashida Abdullahi Adamu - wacce aka fi sani da Rashida mai sa'a - ta ce sabon mukaminta ba zai hana ta shiga harkar fina-finai ba, domin daga nan ta soma.

Fitacciyar jarumar ta ce za ta yi amfani da sabon mukamin nata ta kawo ci gaban matan jihar Kano musamman ta fuskar ilimi da sana'a da kuma kyautatawa marayu.

Ta kuma ce za ta kawo ci gaban masana'antar shirya fina-finan ta Kannywood inda ta fito.

Rashida ta yi fina-finai da dama wadanda yawancin su ita ta shirya, ta dauki nauyi da kasuwancinsu.