Akwai wuya yaki da kungiyar IS - Obama

Hakkin mallakar hoto Islamic State
Image caption Mayakan IS sun ce babu gudu babu ja da baya

Shugaba Obama ya ce yaki da kungiyar masu da'awar kafa kasar musulunci ta IS na ci gaba da zama mai wahalar gaske.

To amma a cewarsa dakarun Amurka na ragargazarsu fiye da yadda ba a zato.

Ya ce dakarun Amurka sun kashe shugabannin kungiyar da dama, kuma sun kai hari kan cibiyoyin man fetur din da suke samu kudaden tafiyar da ayyukansu.

Obama ya ce kuma aminan Amurka ta kasa, na hura musu wuta a Syria da Iraki.

Mr Obama na magana ne a wani taron manema labarai, da ba safai ake irinsa ba a ma'aikatar tsaro ta Pentagon a kan kokarin da Amurka ke yi na murkushe kungiyar IS.

Jawabin na zuwa makonni biyu bayan da wasu mata da miji suka kashe mutane 14 a California.