Jahilci na janyo tsattsaurar akida — Bugaje

Masana a Afrika sun danganta karancin ilimi a matsayin daya daga cikin dalilan da ke haddasa tsattsauran ra'ayin addini a nahiyar.

Matsalar tsattsaurar akidar musulunci tsakanin mabiya, a lokuta da dama tana janyo rigingimu da kan kai ga asarar rayuka.

Masanan sun yi tsokacin ne a wajen wani taro da gidauniyar Carter Center ta shirya a makon jiya a birnin Accra na kasar Ghana.

Dakta Usman Bugaje na wata cibiyar bincike a Najeriya ya ce hukumomi ba sa mai da hankali ga bunkasa karatun addinin musulunci kamar yadda ake yi wa na boko.

Ya ce idan aka rika bai wa karatun addinin muhimmanci a Afirka, hakan zai taimaka wajen fahimtar da mabiya addinin musanman matasa ainihin koyarwar addinin.

Mahalarta taron sun kuma yi nazari akan cin zarafi da ake yi wa mata tare da lalubo hanyoyin magance kuskuren fahimtar koyarwar addini a kan batutuwan da suka shafi rayuwar mata a Afrika.