Saudiyya: Za a kafa sabuwar hadakar soji

Hakkin mallakar hoto .

Kasar Saudiyya ta sanar da kafa wata sabuwar hadakar dakarun soji tsakanin kasashe 34, akasari kasashen Musulmai domin yaki da ta'addanci.

Kamfanin dillancin labaran kasar SPA, ya ce daga birnin Riyadh na Saudiyya za a rika tsara ayyukan dakarun kawancen.

Kasashen dake cikin hadakar, daga yankunan Larabawa, da Asiya ta Kudu da kuma Afirka.

Da yake magana a wajen wani taron manema labarai, yarima mai jiran gado, Mohammed Bin Salman ya ce hadakar dakarun za ta yaki kungiyoyin masu tsattsaurar akida a Iraqi, da Syria, da Libya da Masar da kuma Afghanistan.

Sai dai babu cikakken bayani game da yadda hadakar za ta tunkari wannan yaki a zahiri.

Kasashen larabawa na yankin Gulf dai na ci gaba da fuskantar matsin lamba akan su kara hobbasa wajen yaki da kungiyar IS a Iraqi da Syria.