An kashe kwamandan sojin Saudiyya a Yemen

Image caption Yemen ta shiga cikin yanayi na rashin tabbas

Wani babban kwamandan rundunar sojin Saudiyya da wani sojan Hadaddiyar Daular Larabawa na daga cikin sojojin kasashen waje da dama da aka kashe a fadan da suke da 'yan tawayen Houthi a Yemen.

Ana ganin an kashe su ne a wani harin da aka kai da makaman roka kan wani sansanin sojin da Saudiyya ke jagoranta a yakin da suke na maido da gwamnatin Yemen.

Wakilin BBC ya ce an kashe sojojin biyu ne a kusa da daya daga cikin wuraren da aka fi fafatawa a yakin Yemen din watau a birnin Taez.

Suma dakarun sojin Sudan na cikin wadanda aka kashe din.

Wannan dai na zuwa gabanin tattaunawar zaman lafiyar da aka shirya yi ranar Talata tsakanin 'yan tawayen Houthin da gwamnatin Yemen.