Turkiyya ta ci tarar Twitter saboda yada farfaganda

Hakkin mallakar hoto Getty

Hukumar kula da sadarwa ta kasar Turkiya ta ci tarar kamfanin shafin Twitter Fam 33,000, saboda zargin shafin da kin cire wata farfaganda ta 'yan ta'adda.

Wannan ne karo na farko da aka ci kamfanin Twitter tara.

Hukumomin Turkiyyan ba su bayar da cikakken bayani game da abin da farfagandar da a ke magana a kanta ta kunsa ba, sai dai BBC ta fahimci cewa ta na da alaka da wani shafi da masu bore na siyasa ke sukar gwamnati.

Kawo yanzu, kamfanin na Twitter bai ce komai ba.

Wannan ba shi ne karo na farko ba da shafin ke shiga matsaloli da hukumomin Turkiyyan.

A cikin watan Afrilu, an rufe shafukan Twitter da Facebook a Turkiyya bayan wani umarnin kotu da ke hana mutane yada hoton wani mai shigar da kara da 'yan bindiga suka yi garkuwa da shi.

A watan Maris na 2014, an bayar da rahoton rufe shafin na Twitter a kasar bayan Firayiministan kasar a wancan lokacin, Recep Tayyip Erdogan ya sha alwashin kawar da Twitter gaba daya.

Hakan kuwa, saboda wasu zarge zarge game da jam'iyyarsa da aka rika yada wa ta shafin kafin zabubbuka.