Tasirin da maganin rage radadi ke yi ga lafiya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bincike ya nuna cewa bai kamata a mayar da magungunan kashe radadi na sha ko yaushe ba.

An yi Allah-wa-dai da babban kamfanin da ya fi samar da maganin rage radadi a duniya, kan yadda yake yaudarar abokan huldarsa a Australia.

Amma me ya sa mutane ke sayen maganin rage radadi a wuraren da ba su dace ba?

Akwai magungunan rage radadi dangogin Nurofen kala daban-daban.

Akwai irin su kafso da na tsotsa da na hadiya.

Wadansu an yi su ne domin magance nau'ukan ciwon kai daban-daban irin su Migraine, wato kamar maganin Nurofen Migraine Pain ko Nurofen Tension Headache.

Amma an umarci kamfanin Reckitt Benckiser mai samar da maganin Nurofen da ya dakatar da samar da irin wadannan magunguna na rage radadi ga kantunan sayar da magani a Australia.

Kotu ta yanke hukunci cewar suna yaudarar abokan ciniki saboda da yadda suke nuna cewa maganin na magance ciwuka daban-daban ne.

A takaice dai wadannan magunguna suna kunshe da babban sinadarin ibuprofen lysine 342mg.

"Biyan bukatar rai"

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An zargi babban kamfanin Reckitt Benckiser da yaudarar mutane wajen sayar musu da maganin rage radadi

Kamfanin Reckitt Benckiser ya ce suna kokarin biya wa mutane bukatunsu ne kawai.

Sun jajirce cewa kashi 88 cikin 100 na mutane na neman magungunan da za su rage musu radadin ciwo ne.

Kamfanin ya kara da cewa suna rubuta aikin da maganin ke yi a jikin kwalin misali, "maganin ciwon baya ko na al'ada" ne saboda su bai wa mutane damar zaben ainihin maganin lalurar da ke damunsu.

Amma ita kotun ta kasar Australia ta ce idan mutum ya sayi maganin ciwon kai na kwibi daya wato Nurofen Migraine Pain ko kuma na ciwon kan gajiya wato Nurofen Tension Headache, tamkar bata kudi ne don kuwa duk magani daya ne a kwalaye daban-daban.

Ko a Biritaniya ma ana sayar da irin wadannan magunguna masu kama da juna, amma gwamnatin kasar bata dauki wani hukunci kan maganin rage radadi na Nurifen ba.

Wata likita a Manchester Farrah Sheikh, ta ce idan mutum ya hadiyi maganin rage radadi kamar ibuprofen, zai yi aiki ne a dukkan jikin ta magudanan jini.

Amma tana ganin cewa magungunan rage radadi da aka yi musamman don magance radadin wani bangare na jiki zai yi aiki ne kawai a bangaren da ke ciwon amma ba zai zagaye illahirin jikin ba.

"Maganin bogi"

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Akwai magungunan rage radadi na bogi.

A wani bincike da aka gudanar a baya-bayan nan, masu bincike sun bai wa mutanen da ke yawan fama da ciwon kai maganin bogi.

Wasu daga cikin magungunan an rubuta a jikin kwalinsu cewa magungunan rage radadi yayin da wasu kuma ba a rubuta ba.

Binciken ya ce wadanda aka rubuta aikinsu a jikin kwalin sun fi aiki sosai kuma ba su cika illa ba fiye da wadanda ba a rubuta aikin nasu a jikin kwalin ba.

"Aikin wasu magungunan da illarsu"

Paracetamol: Amfaninsa shi ne magance ciwon kai da ciwukan da suka danganci jijiyoyi.

Ba a cika samunsa da illa ba, amma shansa ya wuce kima na jawo mummunar illa.

Idan dai har ciwon ya wuce kwanaki uku bai gushe ba, to gara a tuntubi likita.

Ibuprofen: Magunguna dangogin ibuprofen da diclofenac da naproxen kuwa sun fi yin aiki ga ciwuka irin su rauni da amosanin gabbai wato arthritis. Bai kamata a yi amfani da su na tsawon lokaci ba sai dai idan akwai kunburi. Idan kuma har aka sha su na tsawon lokaci to akwai yiwuwar ya jawo ciwon ciki ko zubar da jini ko ciwon koda ko kuma ciwon zuciya.

Aspirin: Shi ma dai illolinsa irin na dangogin ibuprofen ne, amma ba shi da karfi sosai wajen rage radadi, wanda hakan ke nufin ba a cika bayar da shi don ya rage radadin ciwo ba, kuma yana da matukar illa ga yara 'yan kasa da shekara 16.