Hanyoyi biyar da sauyin yanayi ke shafar Afrika

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sauyin yanayi yana matukar barazana ga harkar noma a Afrika

Wakilai daga kasashe 196 sun yi ta musayar ra'ayoyi a lokacin taron sauyin yanayi na duniya a Paris, inda a karshe suka cimma yarjejeniya kan lamarin domin ceto duniya daga illolin dumamar yanayi.

Kasashen Afrika 44 duk sun tsaya a kan magana daya, inda suka yi kira da a cimma yarjejeniya kan a rage dumamar yanayi da maki 1.5 na matakin selshiyos zuwa karshen wannan karni.

Wannan buri dai ya fi na baya da ake son cimma na rage maki biyu a matakin selshiyos.

Ana zaton Afika za ta zamo daya daga cikin nahiyoyin da sauyin yanayi zai yi wa barazana, duba da yadda ake samun karuwar fari da ambaliya da ruwan sama mai tsanani da suke yi wa lafiyar al'ummar yankin da kuma tattalin arziki barazana.

A cewar hukumar da ke yin nazari kan sauyin yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya IPCC, duba kan yanayin kasa ne ya nuna irin barazanar da Afrika ke fuskanta, wadda ita ce nahiyar da take da matukar zafi, kuma ana tunanin zafin zai karu da maki 1.5 fiye da yanayin duniya.

Kazalika, maganar ba wai ta inda mutane ke zaune ba ce kawai, a'a, ana ma magana kan ko ma sun shiryawa abin da zai zo nan gaba.

Daya daga cikin mutane hudu da ke zaune a yankin kudu da hamadar sahara na cikin tsananin talauci, miliyoyin mutane basu da galihun samun kudaden da za a kula da su kamar irin na kasashe masu arziki.

Ganin cewa Afrika ba ta tagazawa wajen tallafawa kan sauyin yanayi, mutane da dama suna ganin za ita ce kurar baya.

Ko da a yau da ake samun cibiyar masana'antu da ba a taba samun irin su ba a nahiyar, Afrika ce ke samar da kashi hudu cikin 100 na gurbatacciyar iska, wadda kwararru ke cewa ita ce silar dumamar duniya.

Ga dai wasu daga cikin bangarorin da IPCC ke hasashen sauyin yanayi zai yi tasiri a Afrika:

1. Noma zai yi wahala

Image caption Tuni dabbobi suka fara mutuwa saboda fari da rashin ruwa a Afrika.

Hukumar da ke kula da sauyin yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya IPCC ta ce tana da tabbas cewa karuwar zafi da ruwan sama da ba a tsammanin irin sa za su sa manoma su sha fama wajen shuka kayan abinci kamar su alkama da shinkafa da kuma masara.

Ga misali, ta yi hasashe cewa nan da shekarar 2050 yawan amfanin gona na masara zai ragu da kashi 30 cikin 100 a Zimbabwe da kasar Afrika ta kudu.

Wani fitaccen masanin kimiyya ya yi amfani da bayanan da IPCC ta fitar inda ya yi hasashen cewa nan da shekarar 2100 kasashen Chadi da Nijar da Zambiya za su iya rasa kusan bangaren noma saboda sauyin yanayi.

Wannan al'amari dai yana da matukar daga hankali ganin cewa kimanin kashi biyu cikin uku na al'ummar yankin kudu da hamadar Saharar Afrika sun dogara ne da harkar noma kuma bangaren noman ne ya fi kawo wa kasashen kudaden shiga.

2. Amma kuma za a samu wasu sabbin damarmakin noma

Idan ana batun noma, sauyin yanayi zai iya hana wani abin amma kuma zai iya bayar da wani abin.

Don haka a yayin da noman masara ke yin wahala a Afrika ta kudu, noman nata zai zo da sauki a kasashen da ke kan tudu irin su Habasha da Kenya da Tanzaniya, duk da cewa dukkan noman kayan abinci dangogin hatsi zai zo da matsala a Afrikar a cewar wani rahoto da IPCC ta fitar a baya-bayan nan.

Kalubalen da bangaren noma zai fuskanta na iya tursasa manoma su gane irin kayan abincin da za su noma.

Idan har sauyin yanayi na nufin babu amfani a noman masara a wasu yankuna, to dole a nemo wa noman rogo ma mafita tunda shi ma baya son tsananin zafi, kuma rahoton ya ce abinci ne da ake cinsa sosai a nahiyar.

3. Tamowa

Rashin abinci wanda yana daga cikin barazanar da sauyin yanayi ke yi, zai yi matukar illa kan lafiyar mutane.

Hukumar IPCC ta ruwaito cewa nan da shekarar 2025 ana sa ran yara 250,000 a Mali za su dinga tsimbirewa da fama da tamowa, kuma duk sauyin yanayi ne zai jawo wadannan matsaloli.

Duk da cewa yawan masu fama da tamowa na raguwa a yankin kudu da hamadar saharar Afrika, to kafatanin yawan ya karu ne saboda yawan haihuwar da ake samu cikin shekaru ashirin da suka gabata.

Nan da shekarar 2050 ana sa ran yawan al'ummar mutanen yankin kudu da hamadar sahara zai ninka da biliyan 1.9. Hakan nufin mutane za su sha fama wajen neman abin da za su kai bakin salati.

4. Malaria

Image caption Fiye da mutane rabin miliyan ne suka mutu a AFrika sakamakon cutar zazzabin cizon sauro a 2013

Hukumar IPCC ta ce yaduwar cututtuka na iya karuwa ko raguwa saboda sauyin yanayi.

Amma ta yi wani hasashe gaba gadi ga yankin gabashin Afrika, wanda yana daya daga cikin yankin da ke da yawan mutane a nahiyar.

5. Karancin ruwa

Daya daga cikin barazanar da nahiyar ke fuskanta shi ne wadda take yi wa masana kimiyya wahalar fayyace wa a kan sauyin yanayi.

Abubuwa da dama na jawo karancin ruwa kamar karuwar al'umma da kaura zuwa birane.

Bayan haka kuma, tuni kasashen Afrika da dama ke fuskantar hadarin rashin isasshen ruwa, kuma an kiyasta cewa kashi 95 cikin 100 na gonakin da ke yankin kudu da hamadar saharar Afrika basa samun isasshen ruwa.

Farfesa Opha Pauline Dube, na jami'ar Botswana ya shaida wa BBC cewa "Ruwa shi ne rayuwa, kuma idan ba ruwa, nahiyar Afrika za ta mutu murus."

A cewar bankin raya Afrika AfDB, nahiyar Afrika dai za ta bukaci dala biliyan 20 zuwa biliyan 30 kowacce shekara nan da shekaru 20 domin magance matsalar sauyin yanayi.