Ghana: An kama dan Burkina Faso da makamai

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da zaben kasar Ghana ke matsowa

'Yan sanda a birnin Kumasi da ke jihar Ashanti a kasar Ghana sun kama wani dan kasar Burkina Faso mazaunin Ghanan da muggan makamai har da na kakkabo jiragen sama da kuma dimbin harsasai.

'Yan sanda dai sun ce mutumin wato Moro Sata, mai shekaru 72 da haihuwa ya shaida musu cewa ana kawo masa makamai da harsasan ne daga kasashen Ivory Coast da Burkina Faso da kuma Nijar.

A hirarsa da manema labarai babban kwamandan 'yan sandan Ghana ya ce mutunen suna amfani da kasar ne a matsayin wata hanya ta jigilar makamai zuwa sauran kasashe da ke yammacin Afrika.

Masana dai a Ghana na ganin irin wadannan al'amura suna da daga hankali yayin da zaben kasar ke karatowa.