El-Zakzaky: Iran ta gayyaci jakadan Nigeria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Iran ta bukaci hukumomin Najeriya su biya 'yan Shi'a diyya.

Hukumomi a Iran sun gayyaci jakadan Najeriya da ke kasar domin ya yi musu bayani kan abin da ya sa sojojin Najeriya suka yi arangama da 'yan Shi'a.

Kamfanin dillancin labaran kasar Iran IRNA, ya ambato ma'aikatar harkokin wajen kasar na cewa an gayyaci jakadan Najeriya ne domin, "Mu bukaci gwamnati Najeriya ta yi karin haske kan rikicin da ya faru, sannan ta bai wa wadanda suka jikkata magunguna, kana ta biya diyya ga wadanda suka mutu."

Kamfanin dillancin labaran na Iran ya ce ministan harkokin wajen kasar Mohammad Javad Zarif, ya yi kira da a gaggauta daukar matakin dakatar da rikicin, a hirar da ya yi da takwaransa na Najeriya Geoffrey Onyeama, ta wayar tarho.

Rundunar sojin Najeriya dai na ci gaba da tsare shugaban 'yan Shi'a, Ibrahim El-Zakzaky, wadda ta yi zargin cewa mabiyansa sun yi yunkurin kashe Babban Hafsan sojin kasa na Najeriya, Janar Tukur Buratai ranar Asabar, ko da ya ke kungiyar ta Shi'a ta musanta zargin.