An rufe makarantun gwamnati a Los Angeles

Image caption Motocin daukar dalibai ba su yi aiki ba

An rufe makarantun gwamnati a yankin Los Angeles na Amurka saboda barazanar tsaro.

Sashin ilimi na Los Angeles ya ce an rufe makarantu fiye da dubu daya abin da ya shafi dalibai kusan dubu 700.

'Yan sanda sun ce an fuskanci barazana ta hanyar na'ura a don haka dole ne a gudanar da bincike a dukkan makarantu.

Barazanar na zuwa ne makonni biyu bayan kisan da aka yi a San Bernardino inda mutane 14 suka rasu.

Wasu masu tsattsauran ra'ayin Musulunci ne suka aikata kisan.