"An kashe 'yan Shi'a sama da 200"

Image caption Har yanzu shugaban 'yan Shi'a Sheikh El-Zakzaky yana hannun jami'an tsaro

Masu fafutukar kare hakkin bil adama a Najeriya sun goyi bayan ikirarin da 'yan Shi'a su ka yi na cewa an kashe mabiyansu sama da 200 a lokacin wani samame da sojoji suka kai a wasu guraransu uku a Zariya.

Chidi Odinkalu na hukumar kare hakkin bil adama ya saka wasu hotuna a shafin intanet da ke nuna yadda manyan motoci ke rusa masallacin kungiyar 'yan uwa Musulmai.

Ya ce hakanan an rusa shi ma gidan shugaban kungiyar Ibrahim El-Zakzaky.

Sojoji sun musanta cewa mutane da dama ne suka mutu amma kuma ba su fitar da adadin wadanda lamarin ya ritsa da su ba.

Gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-- Rufa'i ya musanta rahotannin da ke cewa matar Sheikh Zakzakyn ta mutu, inda ya ce ana kula da lafiyarta da mai gidanta.

A ranar Talata ne daruruwan 'yan Shi'a a wasu garuruwan arewacin Nigeria suka gudanar da muzahara domin nuna adawa da matakan da sojoji suka dauka a kan 'yan kungiyar a Zariya.

Rahotanni sun ce mabiya shi'a sun yi zanga-zanga a Kaduna da Kano da Sokoto da Bauchi da kuma Zamfara.