Shugabannin kasashe suna saurin tsufa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Furfura

Wani bincike game da lafiyar shugabannin kasashe da Firayiministoci ya nuna cewa shugabannin suna saurin tsufa, sannan kuma suna rasa shekaru uku na nisan rayuwarsu.

Masu binciken sun yi nazari akan shugabanni 279 a kasashe 17.

Sun yi nazarin rayuwar shugabannin don gano a shekaru nawa suke mutuwa idan aka kwatanta da abokan hamayyarsu da suka sha kaye a zabuka wadanda basu taba rike mukamin shugaban kasa ba.

Likitocin sun ce sakamakon binciken na su, ya nuna cewa gajiyar da aikin shugabanci ke kawowa, ta na sa wadanda suka shugabanci kasashensu saurin mutuwa.