An 'kori' 'yan Boko Haram daga Sambisa

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Rundunar sojin ta ce ta lalata sansanoni hudu a dajin Sambisa.

Rundunar sojin Najeriya ta yi ikirarin korar 'yan kungiyar Boko Haram daga sansanoni hudu da ke dajin Sambisa.

Dajin na Sambisa dai shi ne babbar maboyar 'yan kungiyar ta Boko Haram, kuma a baya, an taba yin zargin cewa a can ne aka boye 'yan matan Chibok fiye da 200 da kungiyar ta sace a watan Afrilun shekarar 2014.

A wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriya, Kanar Sani Usman Kukasheka ya aike wa gidajen watsa labarai, ya ce "Dakarunmu sun kawar da 'yan Boko Haram daga yankin Aulari wanda ke cikin dajin Sambisa. An latata dukkanin sansanoni hudu da ke cikin dajin, wadanda suka hada da Faldan, Kidiziromari, Kuroshini, Kurumari da kuma Ngulda."

A cewarsa, an kashe wani dan Boko Haram wanda ke kokarin tserewa, sannan aka ceto mutane 31.

Kukasheka ya ce dakarun runduna ta 7 ta sojin Najeriya sun yi shawagi a yankin Leje, kuma sun lalata kauyuka kusan 15 da ke yankin.

A cewarsa, kauyukan su ne:Khadadamamari, Ladin Buta, Hilmari, Kashauri, Keshan Ngala, Aiwa, Masu Kura, Mabirni, Grza 1 da 2, Mashuari, Dubenge, Tauba da kuma Majande.