Shi'a: Amurka na so a yi sahihin bincike

Hakkin mallakar hoto MEHR
Image caption El-Zakzaky na hannun jami'an tsaro

Gwamnatin Amurka ta nuna matukar damuwarta kan rahotannin tashin hankali tsakanin jami'an tsaro da mabiyar Shi'a a Nigeria.

Sanarwa daga ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja, ta bukaci gwamnatin Nigeria ta gudanar da sahirin bincike kan lamarin da ya auku a Zariya sannan a hukuncin wadanda suka aikata laifi.

Ita ma kungiyar kare hakkin dan-adam ta Amnesty International ta yi kiran a gudanar da bincike mai zurfi don gano adadin mutanen da suka rasa rayukan su a lamarin.

Kungiyar ta ce kawo yanzu ba ta samu cikakken bayani ba, game da adadin mutanen da aka kashe.

Shugaban kungiyar ta Amnesty International a Nigeria, Ambasada Muhammad Kawu Ibrahim ya ce ya za ma wajibi a hukunta duk bangaren da aka samu da laifi a lamarin domin hana sake aukuwar haka a gaba.

Ya ce dole ne a bai wa wadanda jami'an tsaro suka kama a lamarin damar yin magana da lauyoyinsu, sannan kuma su samu kulawa ta musanman daga jami'an kiwon lafiya.

Ita ma kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta buka ci a gudanar da bincike don gano wadanda ke da laifi a arangamar.

Shugaban kungiyar Farfesa Ango Abdullahi ya ce kungiyar ta damu matuka da kashe-kashen da aka samu, sannan ya ce wannan ba shi ne karo na farko ba da irin haka ke faruwa a kasar.

Farfesa Abdullahi ya ce tawagar da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya aika don duba abin da ya faru ta yi kadan, inda ya ce kamata ya yi shugaban kasa ya ce zai kafa hukumar bincike game da lamarin.

'Tawagar gwamnatin tarrayya'

Tun da farko dai, Shugaba Buhari ya aika da tawagar manyan jami'an gwamnati da na tsaro zuwa Kaduna da Zaria domin ganin halin da ake ciki, sannan su gabatar masa da rahoto kan abin da ya auku.

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Kaduna, ASP Zubairu Abubakar, ya yi wa wakilinmu, Nura Mohammed Ringim karin bayani kan ziyarar:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti