Kotu ta jaddada soke zaben gwamnan Rivers

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption A ranar 11 ga watan Afrilu ne aka gudanar da zaben gwamnan Rivers, wanda masu sa ido suka ce an tafka magudi.

Kotun daukaka kara a Najeriya ta jaddada hukunci da wata kotun sauraron korafe-korafen zabe ta yanke na soke zaben gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike.

A watan Oktoba ne kotun sauraron korafe-korafen zaben ta soke zaben gwamnan wanda aka gudanar ranar 11 ga watan Afrilun 2015.

Kotun ta bai wa hukumar zabe ta kasa INEC umarnin gudanar da sabon zaben gwamna a jihar cikin kwanaki 90.

Hakan ya biyo bayan korafin da jam'iyyar APC da kuma dan takararta Dakuku Peterside, suka gabatar inda suke zargin cewa zaben yana cike da magudi.

A yayin da take jaddada hukuncinta, kotun daukaka karar ta warware abubuwa bakwai da Wike ya gabatar, wadanda suka yi wa APC da dan takararta Mista Peterside dadi.