Kotu ta sauke shugaban PDP daga mulki

Image caption PDP ta kwashe shekaru goma sha shida tana yin mulkin Najeriya.

Wata babbar kotun Abuja, babban birnin Najeriya ta sauke shugaban jam'iyyar PDP na riko, Uche Secondus, daga kan mukaminsa.

Wadansu 'ya'yan jam'iyyar ne karkashin jagorancin tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin siyasa, Ahmed Gulak, ne suka kai shi kara, inda suka bukaci a sauke shi saboda ya fito ne daga yankin kudancin kasar, sabanin kundin tsarin mulkin jam'iyyar da ya ce dan yankin arewacin kasar ne ya kamata ya zama shugaban jam'iyyar.

Alkalin kotun Huseini Baba-Yusuf ya ce Secondus yana kan kujerar shugabancin jam'iyyar ne ba bisa ka'ida ba.

Sai dai Mista Secondus ya ce zai daukaka kara.

Da ma dai rikicin shugabancin jam'iyyar ya barke ne bayan saukar da shugabanta, Ahmed Adamu Mu'azu, wanda dan arewacin Najeriya, ya yi daga mulki, kana aka bai wa Secondus rikon kwarya, lamarin da Alhaji Gulak ya ce ya sabawa dokar jam'iyyar.

Kazalika, jam'iyyar na ci gaba da fama da rikice-rikice tun bayan da ta sha kaye a hannun jam'iyyar APC a babban zaben kasar na shekarar 2015, ko da ya ke ta sha cewa za ta gudanar da sauye-sauye domin sake kwace iko.