'Yan Shi'a sun yi watsi da kwamitin bincike

Kungiyar 'yan Shi'a a Najeriya ta yi watsi da kwamitin da aka ce babban sufeton 'yan sandan kasar ya kafa domin ya binciki tashin hankalin da aka yi a Zariya.

Haka kuma kungiyar ta yi kira ga hukumomin kasar, su mika mata shugabansu Malam Ibrahim El-Zakzaky da yanzu haka yake hannun sojoji.

Malam Yakubu Yahaya Katsina, daya daga manyan shugabannin 'yan Shi'a a kasar, shi ne ya bayyana wa wakilinmu, Yusuf Ibrahim Yakasai, matsayinsu kan wannan bincike da gwamnati ke shirin yi.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya aika da tawagar manyan jami'an gwamnati da na tsaro zuwa Kaduna da Zaria domin ganin halin da ake ciki, sannan su gabatar masa da rahoto kan abin da ya auku.

Tuni kungiyar dattawan arewacin Najeriya ta bukaci a gudanar da bincike domin gano wadanda ke da laifi a kashe 'yan Shi'a sakamakon rikici tsakaninsu da sojoji.

Kakakin kungiyar, Farfesa Ango Abdullahi ya ce kungiyar ta damu matuka da kashe-kashen da aka samu, sannan ya ce wannan ba shi ne karo na farko ba da irin haka ke faruwa a kasar.

Ita ma gwamnatin Amurka da kuma kungiyar Amnesty International duk sun bukaci a gudanar da sahihin bincike a kan lamarin.