Zanga-zangar adawa da Zuma a Afrika ta Kudu

Image caption Gwamnatin Afrika ta Kudu ta yi watsi da zarge-zargen

Dubban masu zanga-zanga na maci a Afrika ta Kudu domin ganin an cire shugaba Jacob Zuma daga kujerarsa.

Zanga-zangar ta yanzu, ta biyo bayan sallamar ministocin kudi su biyu a mako guda a Afrika ta Kudu, abin da ya janyo rashin tabbas ga tattalin arzikin kasar.

Matakin ya biyo bayan zarge-zargen cin hanci da kuma batun rigima kan mulki a jam'iyyar ANC.

Masu yin macin na amfani da maudu'in #ZumaMustFall a shafukan zumunta na zamani.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar na zargin Mr Zuma da cin amanar tsohon shugaban kasar Nelson Mandela wanda ya sadaukar da kai saboda 'yan kasar.

Sai dai gwamnatin Afrika ta Kudu ta yi watsi da zarge-zargen.