AU ta gargadi gwamnatin Burundi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana kisan dauki dai-dai a Burundi

Kungiyar Tarayyar Afrika - AU ta yi gargadin cewa, ba za ta bari a aiwatar da kisan kare dangi a kasar Burundi ba, inda a 'yan watannin da suka gabata ake samun tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na twitter, kungiyar Tarayyar Afrika ta ce, akwai bukatar a dauki matakan gaggawa domin dakatar da kashe-kashen.

Ana dai gudanar da wani zama na musamman na hukumar Majalisar Dinkin duniya mai sa ido kan kare hakkin bil adama a Geneva, domin tattaunawa a kan rikicin.

Manyan jami'an majalisar dinkin duniya da suka hada da Sakatare Janar na Majalisar Ban-Ki Moon, duk sun nuna damuwar cewa, kasar ta Burundi na kokarin afkawa yakin basasa.

An dai fara zubar da jini ne a kasar a watan Afrilun bana, bayan shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya ce zai sake takara na uku a kasar.