Za a yi bincike kan rikicin Shi'a — El-Rufai

Gwamnan jiihar Kaduna Nasir El Rufai
Image caption Gwamnan jiihar Kaduna Nasir El Rufai

Gwamnatin jihar Kaduna da ke Najeriya ta ce za ta kafa kwamitin binciki da za a dora wa alhakin gano musababbin abin da ya faru a Zaria tsakanin 'yan Shi'a da sojoji.

Gwamnan jihar Nasir El Rufai - wanda ya sanar da haka a jawabin da ya gabatarwa alummar jihar - ya kara da cewa a cikin makwanni biyu masu zuwa ne za a sanar da sunayen mambobin kwamitin.

Malam El Rufai ya kara da cewa daga yanzu gwamnati ba za ta ci gaba da barin wasu kungiyoyin addini ko na jama'a suna tare hanyoyi, kamar yadda 'yan Shi'a ke yi.

Ya kara da cewa shugaban 'yan Shi'a wanda aka kama, Ibrahim El-Zakzaky, ya gina hedikwatar kungiyar wacce aka fi sani da Hussaniyya ba tare da amincewar gwamnati ba.

Gwamnan jihar ta Kaduna ya bukaci mazauna jihar da su ci gaba da yin biyayya ga dokoki, yana mai cewa rashin yin hakan ne ke kawo irin matsalolin da aka fuskanta tsakanin sojoji da 'yan Shi'a.