An kama manyan jami'an sojin Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an tsaron Nijar a bakin aiki

Jami'an tsaro a Jamhuriyar Nijar sun kama akalla manyan jami'an soji hudu sakamakon wasu alamu da aka gano na yiwuwar tashin hankali a kasar, watanni biyu kafin a gudanar da zabe.

Majiyoyin soji sun ce an kama jami'an ne a ranar Talata.

Daga cikin wadanda ake tsare da su akwai tsohon shugaban rundunar soji, Janar Souleymane Salou da Laftanal Kanal Dan Haoua, shugaban sansanonin sojin sama a Niamey, babban birnin kasar.

Hukumomin Nijar ba su bayar da wani dalili na kamun ba.

An ambato wani dan uwan Janar Salou yana cewa, "An ce ana zarginsu da neman haddasa rigima, amma har yanzu babu wani karin bayani kan hakan."

A ranar Talata ne gwamnatin kasar ta tsayar da ranar 21 ga watan Fabrairu a matsayin ranar zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki.