Nijar 'kasar da aka fi wahalar rayuwa a duniya'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Galibin yara a Nijar ba sa kammala karatun sakandare

Wani rahoto da hukumar bunkasar al'umma ta majalisar dinkin duniya ta fitar, ya nuna cewa kasar Nijar ce inda aka fi fuskantar wahalhalu na rayuwa a duniya.

Binciken ya yi amfani da tsawon rayuwa da samar da Ilimi da kuma kudaden da ake samu na yau da kullum wajen auna jin dadin rayuwa.

Rahoton ya ce daga cikin kashi 70 cikin 100 na yara a Nijar da ke zuwa makarantar Firamare, kashi 15 cikin 100 ne ke ci gaba har zuwa sakandare.

Binciken ya saka kasashen Jamhuriyar Afrika ta tsakiya da Eritrea da Chadi da kuma Burundi a can kasa a jadawalin kasashen da ake fuskantar wahalar rayuwa.

Daga cikin kasashe 188 da aka gudanar da bincike a kansu, Norway ce ta zo kan gaba a matsayin kasar da mutum zai fi jin dadin rayuwa.