"An yi yunkurin juyin mulki a Nijar"

Shugaba Muhammadu Issufu
Image caption Shugaba Muhammadu Issufu

Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mahamadou Issoufou ya ce dakarun gwamnatin kasar sun dakile wani yunkurin juyin-mulki da aka yi wa gwamnatinsa.

A wani jawabin da ya yi ta Talabijin, shugaban kasar ya ce masu juyin-mulkin sun yi shirin amfani da jiragen yakin kasar ne wajen tilasta masa sauka daga karagar mulki.

Kafafen yada labaran kasar sun ruwaito cewa an kama wasu sojoji da jami'an gwamnati, kuma ba a fadi dalilin tsare su ba.

A shekara ta 2011 ne aka zabi Mahamadou Issoufou a matsayin shugaban Nijar, kuma yana shirin sake tsayawa takara a watan Fabrairun badi, a zaben da aka ce har an fara ta da jijiyar-wuya.