Shi'a: Sarki Sanusi ya bayar da shawara

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ce bai kamata kungiyoyin addini su rika keta dokokin kasa ba, yana mai karawa da cewa bai kuma kamata hukumomi su yi amfani da karfin da ya wuce kima kan 'yan kasar ba.

Sarkin na Kano ya bayyana hakan ne a wajen wani taron addu'o'i na musamman da ya jagoranta, a daidai lokacin da ake yin zaman zulumi bayan kisan da sojojin kasar suka yi wa 'yan Shi'a, wadanda, a cewarsu, suka yi yunkurin kashe Babban Hafsan Sojin kasa na Najeriya, Janar Tukur Buratai a karshen makon jiya.

Sarki Muhammadu Sanusi II ya ce kamar yadda ya ke babu wata kungiyar addini da za ta mayar da kanta hukuma, su ma jami'an tsaro bai kamata su rika bude wuta a kan kowane irin laifi ba.

Sarkin ya buka ci kungiyoyin addinai da su zamo masu da'a, da kaucewa tsokano fitina saboda ba a san karshenta ba, sannan gwamnati kuma ta rika jan hankalin jami'an tsaro da su rika hakuri kadan, saboda a takaita salwantar rayuka:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Baya ga matakin da sarkin Kano ke bukatar a dauka, wasu malaman addinin Musulunci na ganin matsalar tamkar gobara ce daga kogi, don haka babban maganin ta shi ne addu'a, tun da dai Najeriya kasa ce da mabiya addinin Musulunci da na Kiristanci ke da yawa.

Daya daga cikin malaman addini da suka halarci taron addu'o'in, Ustaz Ya'u Husaini Dodo ya yi kira ga shugabanni a matakai da ban daban da su rika nada masu basu shawara kan sha'anin addini saboda kaucewa irin haka a gaba.

Su kuwa wasu masu fashin bakin al'amura na ganin wajibi ne a koma bin dokokin kasa, sannan kuma shugabanni su rika amfani da bayanai a duk lokacin da za su yi wani abu da zai iya hadawa da mu'amala da jama'a.

Majalisun dokokin tarayyar Najeriya ma sun kafa kwamitoci domin su binciki arangamar da ta auku tsakanin sojoji da 'yan kungiyar Shi'a a kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Majalisun sun yanke shawarar kafa kwamitocin ne a zaman da su kayi na sirri.