An kashe 'yan tawayen PKK 23 a Turkiyya

Image caption 'Yan sisayar kasar sun ce ana kai hari a kan fararen hula.

Hukumomi a Turkiyya sun ce dakarun tsaron kasar sun kashe mambobin kungiyar Kurdawa ta PKK su 23 cikin kwanaki biyun da suka kwashe suna kai samame akansu a yankunan Cizre da Silopi da ke kudu maso gabashin kasar.

An sanya dokar hana fita yayin da aka tura tankokin yaki wasu yankunan.

Rahotanni sun ce wasu magoya bayan PKK sun kakkafa shingaye tare da haka ramuka a dukkan biranen, inda suka mayar da unguwannin yankin wani filin-daga.

An tura kimanin sojoji dubu 10 domin kwantar dakile duk wata barazana da ka iya tasowa.

Firai ministan Turkiyya , Ahmed Davutoglu ya lashi takobin kakkabe 'yan bindigar PKK daga kowanne sako na kasar.

'Yan sisayar kasar sun ce ana kai hari a kan fararen hula.