Amurka ta zargi iYogi da yin zamba

Hakkin mallakar hoto Reuters

Amurka ta zargi daya daga cikin manyan kamfanonin ta ke ba da tallafin kwararru, wato iYogi da matsa wa abokan hulda sayen manhajar da ba sa bukata.

A cikin wata kara da gwamnatin kasar ta shigar a Washington, ta zargi kamfanin iYogi da amfani da wasu dabarun tsorartarwa domin yaudarar abokan hulda.

Kazalika an zargi kamfanin da ikirarin cewa yana da alaka da kamfanin Microsoft da Apple da kuma HP.

Sai dai kamfanin ya musanta wadannan zarge-zarge, yana mai cewa karya ce tsagwaronta.

Kamfanin ya shaida wa BBC cewa "Har yanzu ba mu samu wani kuka a hukumance ba, sai dai bisa nazarin rahotannin da ake yadawa a kafafen yada labarai, dukkan zarge-zargen babu gaskiya a cikinsu".

Kamfanin ya kara da cewa ya san cewa Amurka ba ta saurara wa zamba ta intanet, kuma a matsayinsa na wanda ya san ya kamata, yana yin bakin kokarinsa wajen hada kai da hukuma domin kauce wa aikata laifi.

Babban lauyan gwamnati Bob Ferguson ya yi zargin cewa kamfanin iYogi ya zambaci dubban Amurkawa mazauna Washington da salonsa na yaudara, yana ikirarin cewa hakan ya saba wa dokar kare abokan hulda.

Ya ce yana neman a yi wa iYogi tarar da ta kama daga $2,000 a kan dukkan laifukan da ya aikata da suka shafi tauye hakkin abokan hulda da kuma tarar $100,000 saboda taka dokar leken asirin jama'a ta komfuta.