AU za ta aika dakaru 5000 Burundi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Rikici ya barke a Burundi ne tun da Shugaba Pierre Nkurunziza ya bayyana aniyarsa ta yin ta-zarce.

Rahotanni daga birnin Addis Ababa na cewa kungiyar Tarayyar Afirka ta amince da wani daftari da zai sa a tura dakarunta Burundi domin kare fararen hula.

A ranar Alhamis ne AU ta yi gargadin cewa ba za ta bari a aiwatar da kisan kare dangi a Burundi ba, inda a 'yan watannin da suka gabata ake samun tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa.

Kamfanin dillacin labaran Reuters ya ambato wani jami'in diflomasiyya yana cewa kwamitin kungiyar mai kula da tsaro da zaman lafiya ya amince a tura dakaru 5000 zuwa Burundi.

Sai dai za a iya tura dakarun ne kawai idan majalisar dinkin duniya ta amince da daftarin.

Majalisar dinkin duniya ta ce an kashe mutane akalla 400 a Burundi tun lokacin da Shugaba Pierre Nkurunziza ya bayyana aniyarsa ta yin ta-zarce a watan Afrilu.