An kori ma'aikacin da ya caje minista a Australia

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption An caje Julie Bishop lokacin da take kokarin tafiya birnin New York.

An kori wani jami'in tsaron filin jirgin saman Australia bayan ya bukaci ministar harkokin wajen kasar, Julie Bishop, ta fita daga kan layin da take domin a caje ta.

Lamarin ya faru ne a watan Satumba a filin jirgin saman Melbourne lokacin da ministar ke kan hanyar ta ta zuwa zuwa birnin New York domin halartar taron majalisar dinkin duniya.

An dakatar da jami'in tsaron da ya caje ta daga aiki, kana aka mayar da shi bakin aiki bayan an ba shi horo kan yadda ya kamata ya rika yin aiki.

Sai dai an kori manyan jami'an tsaron da suka ba shi umarnin ya caje ta.