Obama ya bai wa dan Nigeria babban mukami

Hakkin mallakar hoto Treasury Department
Image caption Tun a shekara ta 2009, Adeyemo ya soma rike manyan mukamai

Shugaban Amurka, Barack Obama ya zabi wani wanda iyayensa 'yan Nigeria ne a matsayin mataimakin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro ta fannin tsimi.

A ranar Talata ne Obama ya nada Adewale "Wally" Adeyemo a matsayin wanda zai rike mukamin.

Shugaban Amurkar ya ce "zan yi amfani da ilimi da kwazon Wally wajen ci gaba da kuma bunkasar shugabancin Amurka ta fannin tattalin arziki a duniya."

Adeyemo wanda ya yi karatunsa a Jami'ar California, ya maye gurbin Caroline Atkinson wacce ta shafe shekaru hudu a kan kujerar.

Mr Adeyemo mai shekaru 34, ya soma aiki ne a fadar White House a matsayin mataimakin Darekta.