Ana kada kuri'ar raba-gardama a Rwanda

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Amurka ta bukaci Mista Kagame da ya sauka daga mulki.

A ranar Juma'a ne al'ummar kasar Rwanda ke kada kuri'ar raba-gardama don gyara kundin tsarin mulkin kasar, wanda zai ba wa shugaba Paul Kagame damar ci gaba da mulki.

Tuni dai majalisar dokokin kasar ta amince da wannan yunkuri, kuma ana sa ran zai samu gagarumin goyon baya.

Mista Kagame dai ya fara ne da jagorancin Rwanda a matsayin ministan tsaro, kana ya zama shugaban kasa bayan ya hambare gwamnatin Juvenal Habyiramana, a shekarar 1994.

Amurka dai ta ce da shi kada ya tsaya takara, tana mai cewa ya kamata ya zama abin koyi a yankinsu.

A wannan shekarar ne shugaban kasar Burundi, mai makwabtaka da Rwanda ya sauya kundin tsarin mulkin kasarsa domin yin ta-zarce, lamarin da ya jefa kasar cikin mummunan rikicin kabilanci da na siyasa.