An soke hukuncin kisa da aka yanke wa sojoji

Hakkin mallakar hoto AP

Rundunar sojan Nigeria ta sanar da soke hukuncin ta hanyar harbi da aka yanke wa wasu sojoji 66.

Yanzu dai sojojin zasu yi zaman gidan kaso na shekaru goma maimakon fuskantar hukuncin kisa.

An dai tuhumi sojojin ne da laifukan da suka haɗa da haɗa baki domin aikata mummunan laifi da kuma, da kuma yunƙurin bijirewa hukuma, da kuma ƙoƙarin aikata kisa.

Sauran laifukan sun haɗa da ƙin bin umarnin hukuma, da kuma nuna halaye da basu dace ba.

Sanarwar da kakakin sojan Kanal Sani Usman Kukasheka ya sanya wa hannu ta kuma ce, bayan ƙorafe-ƙorafe da aka gabatar wa babban hafsan sojan, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai ne aka sake duba batun baki daya.

Dan haka ne ma a ƙarshe, aka soke hukuncin kisan, aka maida shi ɗaurin shekaru goma.

Yayin ya ƙi da Boko Haram a baya dai sojoji da dama a jihar Borno sun yi bore, inda suka yi ƙorafin cewa, ana tura su bakin daga ba tare da an samar musu kayan aiki da suke buƙata ba.

Saurari karin bayani:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti