Haiti: Masu Bore sun kona gine-ginen Gwamnati

Ana bore a Haiti Hakkin mallakar hoto AP

Masu bore ko zanga-zanga a kasar Haiti sun cinna wa wasu gine-ginen gwamnati da dama wuta, sun kuma ba wa hamata-iska da magoya bayan shugaban kasar, Michel Martelly bayan an wallafa sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar watanni biyu da suka wuce.

Magoya bayan 'yan adawa sun ce an tabka magudi a zaben, saboda bai kamata a fitar da sakamakon zaben ba gabannin gudanar da bincike.

Nan da makwanni biyu masu zuwa ne za a yi zaben shugaban kasa a Haiti.

Dantakarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa, Jude Celestin ya yi barazanar janyewa.